Friday, December 5
Shadow

Yanda na yi turin baro a kasar Ingila duk da cewa ni likita ne a Najeriya>>Inji Dr. Kelvin Alaneme 

Wani likitan Najeriya da ya koma da zama a kasar Ingila me suna, Dr. Kelvin Alaneme ya bayar da labarin yanda ya karkare da turin bari a kasar Ingila.

Yace a shekarar 2019, ya jw kasar Ingila duk da shi likita ne a Najeriya amma bai samu lasisin yin aikin likitanci a kasar Ingilar ba.

Yace haka suka hadu shi da wani abokinsa me suna Surya suka rika neman yanda zasu yi tare.

Yace kudinsa na karewa kuma gashi yana bukatar ya mayar da iyalansa zuwa Ingila, yasan cewa idan bai samu aikin yi ba akwai matsala.

Yace a haka wata rana ya kira Surya yace tunda dai aikin ofis ya ki samuwa su je su nemi koma wane irin aiki ne su yi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ministan Wutar Lantarki ya gayamin wutar ta inganta>>Shugaba Tinubu

Yace haka suka rika bi shago-shago suna tabayar ko zasu samu aiki amma ana ce musu babu.

Yace sun kusa kammala titin gaba daya sai suka shiga shagon wani dan kasar Pakistan, inda ya ji dadin labarinsu ya musu tambayoyi inda a karshe yace ya daukesu aiki.

Yace anan ne ya fara aiki duk da kudin ba yawa amma suna samun abinci da kuma kyautuka.

Yace daga nan ne sai suka koma aikin koyarwa wanda shi albashin yana da kyau ba laifi.

Yace daga nan kuma har ya samu ya mayar da iyalansa zuwa kasar Ingila.

Yace babu wani aiki da za’a ce wai mutum dan ya kammala makaranta kada yayi, yace kawai dai a gida Najeriya ana kallon wasu ayyukan da kaskanci, yace amma idan mutum bashi da yanda zai yi, yana iya yinsu dan ya samu rufin asiri tunda ba dawwama zai yi yana yi ba.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: An gano cewa, Kwankwaso da Peter Obi Tinubu sukawa aiki a zaben 2023 kuma akwai yiyuwar a 2027 ma zasu sake masa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *