Friday, December 5
Shadow

Yanda ‘yansanda suka min fàdè a bakin boda>>Wata ‘yar Najeriya data je cirani kasar Libya ta dawo da kyar ta bayar da labari

Wata ‘yar Najeriya data je Cirani kasar Libya ta dawo da kyar ta bayar da labarin irin wahalar data sha.

Matar sunanta Olaonipekun Adenike kuma shekarunta 30 tana da ‘ya’ya 2.

Tace ita kadai ce a wajen mahaifiyarta dan duk ‘yan uwanta sun mutu.

Tace ta so yin karatu har ta fara amma rashin kudi yasa dole ta hakura.

Tace ta hadu da wata kawar mahaifiyarta a facebook wadda take zaune a kasar Libya wadda ta tambayeta abinda take yi inda ta zayyana mata komai, tace daga nan ne sai kawai magaifiyartata tace mata zata taimaketa musamman saboda irin kirkin da mahaifiyarta ta mata lokacin suna tare.

Tace ta shirya ta je Libya aikatau. Tace ta ji dadin hakan inda suka tashi daga garinsu, Sagamu dake jihar Ogun suka tafi Libya.

Karanta Wannan  Duk me cewa, bamu zaman Aure, yawa kansa Arziki>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Kilishi

Tace sun je Legas suka je Kano suka shiga Nijar, tace acanne suka hadu da ‘yan kasashen Togo, Ghana da sauransu.

Tace daga nan suka kama hanyar zuwa libya, tace sun sha wuya, sai sun roki abinci da ruwa, wani lokacin ma fitsarinsu suke sha.

Tace wasu sun mutu a hanya.

Tace akwai iyakar wata kasa da suka je, sai ‘yansanda suka rika daukar su daya baya daya suna musu fyade, tace amma ba zaya iya tuna iyakar wace kasa bace.

Tace da suka Libya sai kawar mahaifiyarta tace mata ta bata lokaci da yawa a hanya dan haka ta sayar da ita zuwa ga wani dan kasar Ghana.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: An Gudanar Da Jana'izar Aminu Dantata A Madina

Daga nan kuma aka canja mata suna zuwa Ibrahim Aishat inda tace aka ce sai ta yi aikin shekara daya da rabi kamin ta fanshi kanta aka kai ta gidan wani balarabe.

Tace balarabenne ya rika ciyar da ita yana bata kayan sawa.

Tace tana nan ta hadu da wata ‘yar Najeriya data taimaketa ta aikawa ofishin jakadancin Najeriya wasikar neman taimakon a mayar da ita gida.

Tace daga nan aka kirata intabiyu aka kuma ce ta je za’a nemeta, daga baya kuma aka nemeta aka ce tace bayananta sun fito.

Tace tana kan hanyar zuwa ofishin jakadancin Najeriyar ne ‘yansanda suka kamata ba tare data aikata laifin komai ba, tace har fili mahaifiyarta ta sayar ta aika da kudi amma ba’a saketa ba.

Karanta Wannan  Dangote ya sake zuwa na daya a cikin bakaken fata na Duniya da suka fi kowane bakar fata kudi, Karanta sauran

Tace wata rana wani dansanda ya ganta tana kuka yace zai taimaketa shine ya kaita wajan wani dan kasar Ghana.

Daga nan kuma aka sayar da ita zuwa wani gidan karuwai inda ta rika karuwanci.

Tace wata rana hankalinta ya kai ta tsallake katanga ta je ofishin jakadancin Najeriyar inda suka kwashe sati biyu a wajan daga baya jirgi ya kwasosu zuwa Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *