Friday, April 11
Shadow

Yansanda Sun Cafke Jami’insu Da Ya yi Barazanar Ramuwar Gayya Kan Kìsàn Mafarauta a Edo

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta cafke Hadaina Dan-taki, wanda ya yi barazanar kai hari ga ‘yan kudu a Arewa, domin daukar fansa kan mafarauta 16 da aka kashe a Uromi, jihar Edo.

Hakan ya biyo bayan cece-kucen da jama’a suka yi akan jami’an bayan wallafa sakon barazanar a shafinsa na Facebook.

Idan zamu iya tunawa dai dan sandan ya yi barazanar kai harin ramuwar gayya ga ‘yan kudancin Najeriya da ke zaune a arewacin Najeriya.

Kalaman Dan-Taki na zuwa ne a matsayin martani ga kashe ‘yan Arewa 16 da aka yi a garin Uromi dake Jihar Edo.

A wani zazzafan tsokaci da ya yi a Facebook ranar Talata, Dan-Taki ya rantse da Allah sai ya rama kisan da aka yiwa al’ummar Arewa, yana mai shan alwashin cewa ‘yan Arewa za su dauki kwakkwaran mataki kan ‘yan Kudu a nan gaba kaɗan.

Karanta Wannan  Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Don ƙarin bayani, za ku iya kallon cikakkun shirye-shiryenmu a kan decodan DStv lamba ta 393, startimes lamba ta 183 , Canal plus Niger @ 288 , da kuma decodan Gotv lamba ta 18.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *