
Rahotanni daga jihar Legas na cewa ‘yansanda sun kama jarumar fina-finan Hausa, Khadija MaiNumfashi.
Rahoton yace kamen da aka mata na da alaka da wani fada da suka yi da kawarta inda kalaman da ta yi akan wani Kabiru legas suka watsu a kafafen sada zumunta.
Rahoton yace Kabiru Legas dinne ya kai korafi wajan ‘yansanda wanda dalilin hakan yasa aka kama jarumar.
Saidai wata kungiyar ‘yan Fim ta nemi a sako Khadija MaiNumfashi saboda a cewarsu, an take hakkinta kuma marainiyace sannan ta shiga harkar fim ta hanyar data dace.