
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yansanda a Jihar Rivers sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da suka fito a yau, Litinin.
Rahoton yace da misalin karfe 9 na safe ne matasan masu zanga-zangar suka fito inda suka ci karo da dandazon ‘yansanda a filin Isaac Boro Park dake birnin na Fatakwal.
‘Yansandan aun gayawa matasan cewa ba zasu barsu su yi zanga-zangar ba amma matasan sun ce sai sun yi.
‘Yansandan sun harbawa matasan barkonon tsohuwa sannan suka bisu da duka ciki hadda ‘yan jarida da suka je daukar lamarin.
Hakanan a babban birnin tarayya, Abuja ma, ‘yansandan sun bankawa matasa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa da suka fito yin zanga-zangar a maitama.
Wannan rana ta Zanga-zangar dai ta zo daidai da ranar ‘yansanda ta Najeriya.
Dan haka ne ma ‘yansandan suka nemi a dakatar da yin zanga-zangar amma wanda suka shiryata suka kiya.