Friday, July 17
Shadow

‘Yansanda sun Tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da ‘yan Jarida suka banka musu barkonon tsohuwa a jihar Rivers da Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yansanda a Jihar Rivers sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da suka fito a yau, Litinin.

Rahoton yace da misalin karfe 9 na safe ne matasan masu zanga-zangar suka fito inda suka ci karo da dandazon ‘yansanda a filin Isaac Boro Park dake birnin na Fatakwal.

‘Yansandan aun gayawa matasan cewa ba zasu barsu su yi zanga-zangar ba amma matasan sun ce sai sun yi.

‘Yansandan sun harbawa matasan barkonon tsohuwa sannan suka bisu da duka ciki hadda ‘yan jarida da suka je daukar lamarin.

Hakanan a babban birnin tarayya, Abuja ma, ‘yansandan sun bankawa matasa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa da suka fito yin zanga-zangar a maitama.

Karanta Wannan  Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna

Wannan rana ta Zanga-zangar dai ta zo daidai da ranar ‘yansanda ta Najeriya.

Dan haka ne ma ‘yansandan suka nemi a dakatar da yin zanga-zangar amma wanda suka shiryata suka kiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *