Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane da take zargi sun shiga jihar ne da nufin yin yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama mutanen a garin Kwanar Dangora, kuma yanzu suna hannun ‘yansanda, bayan da ya ya ce sun shiga jihar da nufin yin garkuwa da mutane.
Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ”wannan kasuwancin fa na satar mutane ba zai yi tasiri a Jihar Kano ba Insha Allah”.
Ya kuma gode wa al’ummar jihar bia addu’o’in da ya ce suna yi a koyause.
Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ba ta cikin jihohin yankin da ke fama da masu garkuwa da mutane, kodayake ana ɗan samu jifa-jifa, amma ba kamar sauran wasu jhohin yankin, da matsalar ta yi ƙamari ba.