
Dan majalisar kasar Amurka, Riley Moore wanda Shugaban kasar, Donald Trump ya wakilta ya zo Najeriya yaga yanda ake Mhuzghunawa Kiristoci kamar yanda suke zargi.
Bayan ziyarar tasa yace a yanzu ‘yan Najeriya gaba daya ne ya kamata a samarwa da tsaro.
Saidai yace duk da haka sun fi damuwa da samarwa Kiristoci tsaro.
Yace ya ji dadin yanda Najeriya ta amince zata yi aiki da kasar Amurka dan samarwa kasar tsaro amma ba a baki kawai abin ya kamata ya kasance ba.
Kamata yayi a tabbatar da abubuwan da aka tattauna a aikace.