
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, Otal da su Atiku suka kama dan yin bikin komawa sabuwar jam’iyyar ADC ya gaya musu cewa taron ba zai yiyu ba.
Su Atiku sun shirya yin taronne a ranar Laraba dan tabbatar da komawa jam’iyyar ADC, saidai awanni kamin taron, Otal din yace musu taron ba zai yiyuba.
Otal din me suna, Wells Carlton Hotel and Apartments a sanarwar da ya fitar yace umarnine daga sama aka basu.
Shahararren dan jarida, Dele Momodu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ana dai zargin jam’iyyar APC na da hannu a lamarin.
Saidai hadakar ta su Atiku tace wannan ba zai hanata cimma burinta ba.