Rarara Ya Bada Kyautar Naira Miliyan Goma Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri
Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 10 domin a tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, Rarara ya jajantawa Gwamna Babagana Zulum, Da mai martaba Shehun Barno a yayin ziyarar da Ya kai musu.
Sannan Rarara ya ƙara jajantawa al’ummar jihar, musamman waɗanda suka yi asara sakamakon ambaliyar ruwan.
A yayin ziyarar jajen, Rarara ya samu rakiyar Hajiya Aysha Humaira, Dak Abdullahi Al-Hikimah, Alan Waƙa, da Onarabul Auawal Ahmed Bakori da sauransu.