
Yarima a masarautar Saudiyya, Alwaleed bin Khalid bin Talal – wanda ya shafe fiye da shekara 20 yana cikin yanayin doguwar suma – an yi bikin cikarsa shekara 36 da haihuwa.
Ranar 18 ga watan Afrilu ce ranar da aka haife shi.
Yariman ya shahara a ƙasashen Larabawa, har an laƙaba masa sunan, “Yarima Mai Barci”.