
A Najeriya a yau Juma’a ne ake sa ran jirgin farko na maniyatan aikin hajjin bana na ƙasar zai tashi zuwa ƙasar Saudiyya.
Hukumar alhazan ƙasar ta ce jirgin farko zai fara jigilar maniyyata 315 na jihohin Imo da Abia da kuma Bayelsa zuwa ƙasar Saudiyya.
Za a ci gaba da jigilar maniyatan daga Bauchi da Kebbi da jihohin Osun da kuma Legas.