
A jihar Jigawa ‘yansanda sun kama wani Ango me suna Auwal Abdulwahab dan kimanin shekaru 20 da abokansa 3 saboda yiwa matarsa fyade har ta mutu.
Rahoton yace kakakin ‘Yansandan jihar, SP. Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace abin ya farune ranar 26/04/2025 a kauyen Tango dake yankin Albasu na karamar hukumar Sule Tankarkar.
Kakakin ‘yansandan yace hakan ya farune kwanaki kadan bayan an musu aure inda ya shiga da abokansa su 3, Nura Basiru, Muttaka Lawan da Hamisu Musa cikin gidansa sukawa matar fyade ta karfin tsiya har ta mutu.
Bincike ya bayyana cewa tun farko amaryar bata amince da aure Auwal ba amma daga baya ta rungumi kaddara.
Kakakin ‘yansandan yace bayan samun rahoton faruwar lamarin sun je da jami’ansu gidan inda suka dauki gawar zuwa Asibitin Gumel inda likitoci suka tabbatar da mutuwar matar.
Yace an mika gawar yarinyar zuwa wajan iyayenta dan a binneta su kuma wanda ake zargin duka an kamasu.
Yace bayan kammala bincike za’a gurfanar da duka wadanda ake zargi a kotu.