
Dan majalisa daga jihar Nasarawa, High Chief Otaru Douglas ya bayyana cewa ana samun yawaitar rashin aurene saboda mata na yadda suna baiwa maza damar su aikata Alfasha dasu.
Yace da matan zasu rika kin yadda ana aikata Alfasha dasu, da mazan sun rika aure.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook ranar 20 ga watan October.