
Matatar man fetur ta Dangote ta bayyana aniyar fara jigilar man fetur da Gas a fadin Najeriya nan da watan Augusta.
Hakan na zuwane yayin da kungiyar direbobin tanka ke barazanar daina jigilar man fetur a fadin Najeriya saboda a cewarsu ba zasu iya biyan sabon harajin da gwamnatin jihar Legas ta kakaba musu na biyan Naira 12500 akan kowacw tanka ba.
Daina jigilar man fetur din direbobin tankar na Najeriya ka iya jefa kasarnan cikin mawuyacin hali na karancin man fetur da tsadarsa.
Matatar ta Dangote tace nan da ranar 15 ga watan Augusta zata fara rarraba man fetur dinta a fadin Najeriya da motocin Dangoten.
Jihar Legas dai ta ce ba gudu ba ja da baya game da shirin nata na karbar Haraji Naira 12,500. Inda tace kungiyar direbobin tankar na karbar kudin da suka kai naira dubu 40 akan kowace tanka babtare da yiwa direbobin aikin komai ba.
Saidai Matatar Dangote tace zata kawo sabbin Tankoki 4000 da zata rika jigilar man dasu a fadin Najeriya nan da watan Augusta.