Monday, March 17
Shadow

Za a ƙara alawus ɗin abinci na sojojin Najeriya zuwa naira 3,000

Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar janar Olufemi Oluyede ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kuɗin alawus na kullum da ake RCA da ake ba sojojin Najeriya, wanda yanzu ake ba su naira 1,500.

Da yake yi wa sojojin sashe na 81 jawabi a Legas, Oluyede ya ce za a ƙara alawus ɗin zuwa naira 3,000 daga wata mai zuwa.

Baya ga ƙarin na RCA, babban hafsan ya ce rundunar sojin ƙasan Najeriya za ta fara ba sojoji lamunin kuɗi a kan kuɗin ruwa na kashi 3, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ba sojoji shawarar su nemi bashin kuɗin, domin a cewarsa biyan ba zai zama musu matsala saboda babu ruwa mai girma a ciki.

Karanta Wannan  Za mu kawo ƙarshen Lakurawa cikin ƙanƙanin lokaci- Hedkwatar tsaro

A game da tsarin gidaje, janar ɗin ya ce za su faɗaɗa shirirnsu na lamunin gidaje a Abuja da Ibadan da Jos da Fatakwal da Owerri da Akwa Ibom.

Ya ce a tsarin, sojoji za su iya samun gida a kan kuɗi naira miliyan 8 zuwa sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *