
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta bayyana aniyar ɗaukar matakin shari’a kan Mustapha Jafaru Kaura, mai taimaka wa gwamnan jihar, Dauda Lawal, kan yada labarai bisa zargin yi wa shugabannin jam’iyyar ƙazafi tare da alaƙantasu da ‘yanbindiga da kuma garkuwa da mutane a jihar.
A cewar wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar bayan taron gaggawa na kwamitin gudanarwar jam’iyyar da aka gudanar a Gusau.
Jam’iyyar ta bayyana kalaman jami’in na gwamnatin Zamfara, Jafaru Kaura a matsayin “kalaman harzuƙa jama’a da ɓata suna.”
APC ta ce Mustapha Kaura ya yi iƙirarin cewa Bello Mohammed Matawalle, ƙaramin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara—ya riƙa haɗa baki da ƴanbindiga a lokacin mulkinsa.
Sanarwar ta ce Kaura a wata hira da aka yi da shi a tashar Maibiredi TV ya zargi Matawalle da karɓar naira miliyan 300 na kuɗin fansa daga tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, domin sakin ɗaliban da aka sace a Kankara a shekarar 2020, amma ya miƙa naira miliyan 30 kaɗai ga masu garkuwar
APC ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa an yi shi ne don ɓata sunan Matawalle.
Jam’iyyar ta kuma ce lauyoyinta na duba yiwuwar gurfanar da tashar Maibiredi TV bisa zargin haɗin baki wajen baza zargin.
Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin kuɗin fansa wadda ta addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro na Najeriya ya shafe shekaru huɗu na mulkinsa yana ƙoƙarin shawo kan matsalar, sai dai har yanzu lamarin ya ci tura.
Haka nan tun bayan sauka daga mulki bayan nasrar Dauda Lawal a zaɓen gwamna na shekara ta 2023, mutanen biyu ba su ga-maciji da juna a siyasance, inda ake samun saɓani tsakanin ɓangarorin biyu a kai a kai.