Wednesday, November 12
Shadow

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi yayi bayani dalla-dalla dalilin da yasa yake son su hada kai dan kayar da Shugaba Tinubu

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan hamayya a ƙasar domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu.

Amaechi – wanda ɗan jam’iyyar APC ne – ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira ƙuncin rayuwa da ƙasar ne ciki.

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Kalaman Amaechi na zuwa ƙasa da wata ɗaya bayan jagororin jam’iyyar APC sun amince da Bola Tinubu a matsayin “ɗan takara ɗaya tilo” a zaɓen 2027.

Sai dai tsohon ministan ya ce har yanzu yanan nan a jam’iyyar APC, kuma ”bai zama dole sai ka goyi bayan gwamnati ba, don kawai kana APC.

”Idan gwamnati tana kassara ƙasa sai kawai ka yi ta tafi, don kana APC, ai kai ma ka sani”, in ji Amaechi.

Tsohon ministan ya ci gaba da cewa ”abu mafi dacewa shi ne ka sanar da gwamnati abin da ya dace, ka sanar da gwamnati abin da ƴan Najeriya ke tsammani daga gare ta”.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya kuma koka kan abin da ya kira yadda yunwa ke kashe ƴan ƙasar, sakamakon wahalhalun tsadar rayuwa da ake ciki.

Karanta Wannan  Karya yake a kafa ya rika zuwa makaranta har ya gama>>Abokin Karatun Ministan Abuja, Nyesome Wike ya karyatashi kan cewa, A mota kirar Mercedes Benz ya rika zuwa makaranta

”A kwanakin baya ina tafiya a gefen titi na ci karo da gawa, mutane na mutuwa, mutane na fama da yunwa, ni kai na ina fama da yunwa”, in ji shi.

Mista Amaechi ya ce akwai masu kallon cewa shi ya kuɓuta daga ƙangin yunwa da ƙasar ke ciki, amma kuma “magana ta gaskiya ita ce ni ma ina cikin yunwar”.

Tsohon ministan ya ce a halin yanzu ba ya son tsayawa takarar shugaban ƙasa, kodayake abu ne mai yiwuwa.

”Domin kuwa tabbas akwai gudunmowar da zan iya bayarwa”, in ji shi.

Muna ƙoƙarin yin haɗaka don samar wa ƙasa sauyi

Mista Amaechi ya ce a shirye yake ya shiga haɗakar da ya bayyana da ”inuwar wasu mutane da suka amince ana kassara Najeriya”.

A baya-bayan nan jagororin adawa a Najeriya, ciki har da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP da kuma LP, Atiku Abubakar da Peter Obi sun bayyana aniyar ɗunkewa domin ƙalubalantar Tinubu a babban zaɓen ƙasar na 2027.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a zaɓen Bola Tinubu a zaɓen 2023, Nasir El-Rufa’i ya faɗi cewa sun yi nisa a ƙoƙarin samar da haɗakar wadda za ta ƙalubalanci shugaba Tinubu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Na taba yin Tusa a gaban Saurayina, cewar wannan matashiyar

Sai dai duk da haka ƴaƴan jam’iyyun hamayya da dama na ƙasar sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, lamarin da ya sanya ake zargin shugaban ƙasar da nufin mayar da ƙasar mai bin tsarin jam’iyya ɗaya.

Rotimi Amaechi ya ce ƙasa ta tsaya cak, ba ta tafiya gaba, don haka ne ya ce wasu ke tuntuɓar juna kan abin da ya kamata a yi domin samar da gyara.

”Muna tunanin idan muka zo muka haɗu, kuma muka ci zaɓe, babu shakka ƙasar za ta samu canji”, in ji shi.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce a lokacin da yake matsayin shugaban ƙungiyar gwamnoni, akwai kimanin yara miliyan 10, amma ya ce a yanzu adadin ya zarce haka.

‘Matsalolin tsaro sun yi yawa a Najeriya’

Tsohon ministan sufurin ya kuma koka kan matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta .

”Har yanzu ana fama da rikicin manoma da makiyaya, ga matsalar ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa”, in ji shi.

Rotomi Amaechi ya ce matsalar yunwa ce ta haifar da rikicin Boko Haram da sauran matsalolin tsaro.

Karanta Wannan  Bamu yadda da dawowar El-Rufai Jam'iyyar mu ba, yazo ne kawai ya cimma burinsa>>Kungiyar Matasan Jam'iyyar SDP

”Na sha faɗa wa mutane cewa rikicin Boko Haram ba magana ce ta bambancin addini ba, ɗimbin mutane sun shiga harka satar mutane domin su samu kuɗi saboda yunwar da suke ciki”, a cewarsa.

Najeriya ta kwashe kimanin shekara 15 tana fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, kuma a baya-bayan nan ƙungiyar na ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare duk da cewa a baya gwamnati ta ce ta yi galaba a kanta.

Haka nan matsalar ƴan fashin daji da ke addabar jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Kaduna na ci gaba da korar al’umma daga ƙauyuka – mutanen da suka kasance babbar hanyar samun kuɗin shiga gare su ita ce noma.

Hukumar kare haƙƙin ɗan’adam ta Najeriya, a cikin wani rahoto ta ce adadin mutum 570 ne aka kashe a watan Afrilun bana.

‘Har yanzu ina da tasiri a jihar Rivers’

Tun bayan saukarsa daga muƙamin Minista ne wasu ke ganin tauraruwar tsohon gwamnan ta fara dusashewa, musamman a jiharsa ta Rivers.

To amma ya musanta hakan, yana mai ƙalubalantar duk mai wannan tunani da cewa ya je jihar ya gani.

”Ka je Fatakwal ka tambaya, tun daga filin jirgi, za ka gane”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *