Za A Shafe Makonni Biyu Ana Buɗe Ayyuka Albarkacin Cikar Shugaban Ƙasa Tinubu Shekaru Biyu A Kan Mulki.

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaban ƙasa Tinubu ya kafa gagarumin tarihin samar da manyan ayyuka masu tasiri a fagen shugabancin Najeriya.
Dan haka, za a shafe tsawon makonni biyu ana buɗe ayyukan da ya yi a Abuja ta fannin tituna, ruwa, da sauran ɗumbin ayyukan raya ƙasa, albarkacin cikarsa shekaru biyu a matsayin shugaban ƙasar Najeriya.