Friday, March 21
Shadow

Za mu bi hanyoyin da doka ta tanada wurin dawo mana da haƙƙinmu – Fubara

Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar Siminalayi Fubara ya ce tun hawansa mulki, ya yi ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma kawo cigaba a jihar, sai dai ƴan majalisar dokokin jihar suna ta kawo cikas ga ƙoƙarin nasa.

Gwamnan da aka dakatar ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar bayan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da shi da mataimakiyarsa na watanni shida saboda rikicin siyarsa da ya ki ci ya ki cinyewa.

Fubara ya ce dukkanin abubuwan da ya yi da matakan da ya ɗauka ya yi su ne bisa rantsuwar da ya sha na kama aiki, inda ya ce hakan ne ya sa bayan da shugaba Tinubu ya shiga tsakani, ya yi gaggawar aiwatar da yarjejeniyar da aka amince ciki har da dawo da kwamishinonin da suka ajiye aiki.

Karanta Wannan  Tsohon Ministan Sadarwa Da Tattalin Arzikin Zamani Farfesa Isa Ali Pantami Ya Ziyarci Hajiya Turai Umaru Musa Yar'adua Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Tsohon Shugaban Kasa, Hajia Dada A Gidanta Dake Abuja

Ya kuma ce ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin hukuncin kotun ƙolin domin dawo da zaman lafiya a jihar, sai dai a cewarsa, a kowane mataki ƙoƙarinsa ya gamu da cikas daga ɓangaren majalisar dokokin jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa duk da rikicin siyasar da ake yi, gwamnan ya ci gaba da gudanar da gwamnati yadda ya kamata, inda ya ce ana biyan ma’aikata albashinsu kuma an ƙaddamar da muhimman ayyukan cigaba a jihar.

Fubara ya buƙaci ƴan ƙasar su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga dokar ƙasa, inda ya ce za su ci gaba da tuntuɓar waɗanda suka dace wajen tabbatar da ɗorewar dimokraɗiyyar a jihar, kuma jihar ta ci gaba da bunƙasa.

Karanta Wannan  Ba abinda ya tara mu anan kenan ba amma Mun ji naki bayanin, ki dakata mu ji daga bakin wanda kike zargi, watau Sanata Godswill Akpabio kamin mu yanke hukunci>>Majalisar Dinkin Duniya ta gayawa Sanata Natasha Akpoti

Siyasar jihar ta Rivers ta damalmale ne tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da magabacinsa, ministan birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike.

Lamarin ya kai ga cewa ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike sun yi barazanar tsige gwamna Fubara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *