Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa a shekarar 2025 za’a samu saukin hauhawar farashin kayan masarufi.
Yace alkaluman hauhawar farashin kayan masarufi zasu yi kasa zuwa kaso akalla 15 cikin 100 inda a yanzu suke a maki 34.8 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana.
Ya bayyana hakane a Abuja ranar Litinin yayin kaddamar da kwamitin kula da kudi inda yace zasu cimma burin samun kudin shiga na Naira Tiriliyan 47.9 da suka saka a gaba a shekarar 2025.
Yace babban bankin Najeriya, CBN ya saka burin rage hauhawar farashin kayan abinci zuwa kaso 15 cikin 100 a cikin shekarar nan kuma zasu dage dan cimma wannan buri.