Wednesday, July 9
Shadow

Za’a samu saukin rayuwa, kayan masarufi zasu sauka kasa>>Inji Gwamnatim tarayya

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa a shekarar 2025 za’a samu saukin hauhawar farashin kayan masarufi.

Yace alkaluman hauhawar farashin kayan masarufi zasu yi kasa zuwa kaso akalla 15 cikin 100 inda a yanzu suke a maki 34.8 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana.

Ya bayyana hakane a Abuja ranar Litinin yayin kaddamar da kwamitin kula da kudi inda yace zasu cimma burin samun kudin shiga na Naira Tiriliyan 47.9 da suka saka a gaba a shekarar 2025.

Yace babban bankin Najeriya, CBN ya saka burin rage hauhawar farashin kayan abinci zuwa kaso 15 cikin 100 a cikin shekarar nan kuma zasu dage dan cimma wannan buri.

Karanta Wannan  An kama Fasto da yin mu'ujizar karya inda yace ya mayar da wata mata me kudi amma sai bayan kwanaki aka ganta tana sayar da Lemun Kwalba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *