
Hukumar kula da wasanni ta kasa, NSC ta bayyana cewa Kasar Dr. Congo ba zata tsallake korafin da aka shigar akanta na maganar saka ‘yan wasan da basu dace ba a wasannin data buga da Najeriya.
Shugaban hukumar, Shehu Dikko ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da gidan Talabijin na Arise TV.
Yace ba wai dan Najeriya bata yi nasara bane yasa yake fadat hakan ba, yace tun kan a buga wasan sun san cewa wasu ‘yan wasan kasar ta Benin Republic basu cancanta da buga wasan ba.
Najeriya dai ta shigar da kara gaban FIFA inda take neman a binciki Dr. Congo kan ‘yanwasanta.