Friday, December 5
Shadow

Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima

Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima.

Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NNPP kuma na kusa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai yi matuƙar wuya Kwankwaso ya haɗa kai da jam’iyyar domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027.

Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels , inda ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna adawa ga Kwankwaso ta hanyar goyon bayan Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, duk da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsige shi.

Ya ce Kwankwaso ba ya buƙatar dogaro da APC a siyasa, yana mai tunatar da cewa ya kayar da jam’iyyar a Kano a baya.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

“Kwankwaso bai taɓa gaya min cewa zai mara wa Tinubu baya a 2027 ba,” in ji shi.

Galadima ya ƙara da cewa babu yadda Kwankwaso zai haɗa kai da APC bayan abin da aka yi a Kano, ciki har da naɗin sarakuna biyu a cikin gari ɗaya, yana mai zargin gwamnatin tarayya nuna goyan baya ga Aminu Ado Bayero domin amfani da shi a zaɓen gaba.

Ya ce duk da haka, Kwankwaso na da cikakken farin jini a Kano saboda ayyukan da ya gudanar a baya. “Shi ya sa mutane suke binsa a siyasa,” in ji Galadima.

Game da shirye-shiryen NNPP a 2027, Galadima ya ce ba a yanke hukunci na ƙarshe ba tukuna, amma ya jaddada cewa, “duk inda kuka same mu, a can gwamnati za ta kasance.”

Karanta Wannan  Yanda Mutanen Karkara suka fi na Birni zuwa aikin Hajjijn bana ya kawo cece-kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *