
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata gina bishiyoyi biliyan 20 a Najeriya a damuna me zuwa.
Ya bayyana hakane a kasar Ethiopia a yayin ziyarar da ya kai kasar bayan kai ziyara yankin da suke noma ya ga irin wannan tsari.
Shettima ya bayyana cewa, dasa Bishiyoyin abune dake bukatar tsarawa da kuma wahala amma idan aka dage za’a iya yi, kamar yanda gashi kasar ta Ethiopia ta yi.
Shettima ya kuma jinjinawa kasar Ethiopia bayan da ta zama kasa me cin gashin kanta ta fannin noman Alkama inda yace a baya suna sayen Alkamar Dala Biliyan $1 duk shekara amma yanzu ta wadacesu har ma sayarwa da makwabta suke.
Yace hadaka tsakanin Najeriya da kasar Ethiopia zai taimaka aosai wajan ci gaban yankin Africa.