
Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar sayar da matatun man fetur mallakin Gwamnati, watau na Kaduna, Fatakwal, da Warri.
Gwamnatin tace zata yi hakanne dan inganta aikin matatun da kuma jawo masu zuba jari Najeriya.
Babban me baiwa shugaban kasar shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wajan wani taro a Kasar UAE.
Matatun man fetur din na Najeriya sun lakume makudan kudade wanda aka ware dan gyarasu amma har yanzu basu aiki yanda ya kamata.