
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya haƙura da kujerar shugabancin ƙasar idan haka ne zai zama silar samar da zaman lafiya a ƙasarsa.
Zelensky ya bayyana haka ne a daidai lokacin da aka cika shekara uku ana gwabza yaƙi tsakanin Ukraine da Rasha.
“Idan kuna so in sauka daga mulki, zan amince. Amma ina so ƙasata ta shiga ƙungiyar Nato,” in ji shi a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai.
Wannan jawabin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya kira shi da “mai kama-karyar mulki ba tare da zaɓe ba.”
“Maganarsa ba ta ɓata min tai ba,” in ji Zelensky wanda aka zaɓa a watan Mayun shekarar 2029.
Zelensky ya ƙara da cewa tabbatar da zaman lafiyae ƙasar ne a gaban shi, amma ba ya tunanin daɗewa a mulkin ƙasar.
Majalisar Ukraine ce ta dai yi dokar hana zaɓe a ƙasar tun bayan da Rasha ta faɗa mata da yaƙi a watan Fabrairun 2022.
Shugabannin ƙasashen turai da na wasu ƙasashen za su yi taro a birnin Kyiv na Ukraine domin nuna goyon baya, tare da haɗin kansu ga ƙasar.