Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kammala ginin jirgin kasan daya tashi daga Fatakwal, Jihar Rivers zuwa Birnin Maiduguri na jihar Borno kamin ya kammala wa’adin mulkinsa.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai jihar Enugu yayin ganawa da dattawa daga yankin kudu maso gabas.
Kakakin shugaban kasar, Mr. Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda yace kuma shugaban kasar yayi Alwashin samar da wata tashar makamashi a jihar Anambra.