Friday, December 5
Shadow

Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027 – Peter Obi

Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027 – Peter Obi.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya tabbatar wa magoya bayansa cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027, kuma ba zai yi fiye da wa’adi guda ba idan ya ci zabe.

Mista Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Peter Obi Media Reports, Ibrahim Umar, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya tabbatar da cewa yana cikin tattaunawar kafa kawancen jam’iyyu, yana mai cewa burinsa shi ne ceton Najeriya daga halin da ta tsinci kanta.

Karanta Wannan  Akwai Yunwa a Najeriya>>Inji Fasto Emmanuel Udofia

“Ban taba shiga wata tattaunawa kan hadin gwiwar tikitin takara da kowa ba, har da Atiku,” inji shi.

“Idan za a samu wata yarjejeniya da za ta takaita wa’adin mulkina zuwa shekaru hudu, zan yarda da ita, kuma zan bar ofis ranar 28 ga Mayu, 2031.

“Idan kawancen ba ya magana ne kan dakatar da kashe-kashen da ake yi a Benue da Zamfara, dawo da tattalin arzikinmu, farfado da masana’antunmu, da ciyar da ‘yan Najeriya, to ku cire ni a ciki,” inji shi.

Obi ya yi alkawarin kawo kwanciyar hankali a kasar nan cikin shekaru biyu da fara mulkinsa.

Dangane da halin da jam’iyyar Labour Party ke ciki, Obi ya ce suna aiki tukuru domin samun sahalewar INEC ga shugabancin Nenadi Usman bisa hukuncin Kotun Koli.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya ta dauki manyan Lauyoyi dan karawa da Gwamnonin PDP a kotu game da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *