Zargin Biliyan biyu ga Kwankwaso: Babu hankali da lissafi a maganar Baffa Bichi – Abba Gida-Gida.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Baffa Bichi martani bisa zarge-zargen da ya fada akan gwamnatin.
A wata hira da manema labarai da ta karade kafafen watsa labarai, an jiyo Baffa Bichi, wanda aka cire shi daga muƙamin sakataren gwamnatin, na cewa an ɗauki matakin ne don ya ki amincewa da ya sahale a rika diban Naira biliyan 2 duk wata ana saka wa a asusun Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya.
A wani taro da kansilolin mazaɓu 484 na jihar a yau Lahadi, gwamna Abba ya ce maganganun da Bichi ya yi “babu hankali da lissafi da aiki da ƙwaƙwalwa a wannan maganar.”
A cewar gwamna Abba, babu hankali a ce gwamnatin sa da ko shekaru biyu bata cika ba amma har a rika cewa ta kwashe dukiyar jihar sama da ta gwamnatin da ta gabata.
Ya ce an baiwa Bichi mukami mai girma amma ya fito ya na wasu malamai ma kazafi da babu hankali a ciki, inda ya ce ya binciki kan sa tare da duba akan dalilin da ya sa aka cire shi.
Ya kuma gargaɗi Bichi da ya daina taba Kwankwaso domin shi shugaba ne adali da ya yi mulkin jihar cikin tsafta ba tare da din hanci ba.
Ya kara da cewa Kwankwaso shugaba ne kuma hakkin ne a kan gwamnatin sa ta kare mutuncin da martabar sa da ma sauran manyan jihar, inda ya ja kunnen ƴan siyasa akan taba muhibbar shugabanni.
Hakazalika gwamnan ya kuma yi gargaɗi ga gidajen rediyo da su guji yada irin waɗannan kalamai, inda ya kara da cewa gwamnatin sa ba za ta amince da hakan ba.