Wednesday, April 29
Shadow

Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya

Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya.

Dr. Mubark Mahmud PhD, mai bincike kan muhalli ya ƙirƙiri sabuwar hanyar auna tsawon bishiya wanda duniyar kimiyya ta karba ta kuma raɗa wa binciken suna “Mahmud Method”.

An saka a manhajar M-Tree da jami’o’i a Faransa ke amfani da ita wajen auna tsayi da kauri na bishiyoyi.

Tuni dai aka ƙaddamar a jami’ar da ya ke karatu, université Paris-Saclay a ranar 30 ga watan Afrilu.

Tuni dai aka wallafa wannan bincike a wata mujallar noma mai suna Smart Agricultural Technology Kuma za a saka shi a manhajojin koyarwa a makarantu da cibiyoyi da dama.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda dan siyasa a jihar Adamawa ya tsere yayin da yaga mutanen mazabarsa na shirin yi masa na jaki

Hakazalika an baiyana cewa akwai shirin za a bunƙasa binciken ta hanyar saka shi a ƙirkirarriyar fasaha wato Artificial Intelligence, AI.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *