
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai wa iyalan sojijin da aka kashe da kuma waɗanda aka jikkata a fagen daga a yaƙi da ƴan ta da ƙayar-baya a arewa maso gabas, tallafin naira miliyan 100.
Gwamnan ya bayar da tallafin ne ranar Asabar yayin liyafar cin abinci a daidai lokacin da ake ci gaba da bukukuwan sallah, inda babban hafsan sojin ƙasa Laftanar-Janar Olufemi Oluyede da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar suka halarci liyafar a barikin sojoji na Maimalari a Maiduguri.
Zulum ya gabatar da chekin kuɗin na naira miliyan 100 ga hannun kwamandan dakarun Haɗin-Kai, Manjo-janar Abdussalam Abubakar.
Ya bayyana cewa kowane soja da aka raunata a fagen daga zai samu naira 500,000, yayin da za a raba sauran kuɗin ga iyalan sojojin da aka kashe.
Gwamna Zulum ya kuma yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewarsu, inda ya ce ba za a taɓa manta irin sadaukarwar da suka yi ba.
“Jajircewarku a fagen daga, duk da irin barazana da kuma wahala ba zai tafi a banza ba. Muna ƙara godiya bisa amanar tsaron ƙasa da kuka ɗauka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mara wa sojojin baya.
“Gwamnatin Borno za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da sojojin Najeriya da kuma dukkan jami’an tsaro a yaƙi da ƴan ta da ƙayar-baya, da kuma sake gina garuruwan mu don samar da zaman lafiya da makoma mai kyau,” in ji gwamna Zulum.