
Rashin zuwa wakilin da kasar Amurka ta turo zuwa Najeriya dan ya duba abinda suke zargi na Khisan Kyiyashi da suka ce anawa Kiristoci zuwa sauran jihohin Najeriya dake fama da matsalar tsaro ya jawo cece-kuce.
Riley Moore wanda dan majalisar kasar Amurka ne kuma me karfin riko da Kiristoci ne Trump ya wakilta ya masa bincike kan lamarin.
Kuma ya zo ya gana da wakilan Kiristoci a jihar Benue amma ba’a ganshi yana ganawa da bangaren musulmai ba, sannan ba’a ganshi a jihohin Inyamurai ba kuma ba’a ganshi a jihar Filato ba inda nan ma ana da matsalolin tsaron.
Saidai wannan bai zowa mutane da mamaki ba lura da cewa, dama can Amurkar tace Khisan Kyiyashi da akewa Kiristoci ne take son hanawa.
Duk da cewa bayan kammala ziyarar tasa, Riley Moore yace akwai bukatar samarwa duka ‘yan Najeriyar tsaro amma yace Kiristoci ne zasu fi baiwa muhimmanci.