Tuesday, January 7
Shadow

Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

Kafofin yaɗa labarai a Nijar da Mali da Burkina Faso sun ruwaito a ranar Litinin cewa ƙasashen za su kafa wata tashar talabijin ta intanet da zimmar “ƙarfafa haɗin kai da kuma yaƙi da labaran ƙarya” a yankinsu na Sahel.

Ƙasashen uku da sojoji ke mulki, sun kafa ƙawance da suka kira Alliance of Sahel States, wanda suke kira da Aes a Faransanci.

“Ana sa ran tashar za ta inganta harkokin sadarwa tsakanin ƙasashen Sahel kuma a samu tasiri mai ɗorewa bisa muradin shugabannin ƙasashen biyu,” in ji rahoton shafin Actu Niger.

An ƙulla ƙawancen ne a 2023 bayan sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas, wadda suka zarga da yi wa ƙasashen Yamma aiki.

Karanta Wannan  CIKIN HOTUNA: Rarara Ya Tallafawa Wasu daga cikin kin manoman Jihar Katsina, da Naira Miliyan Ashirin ( 20,000,000 ) Domin Suyi Chefanen Babbar Sallah

Nijar da Mali da Burkina duka sun yanke alaƙa da ƙasashen Yamma kamar Faransa kuma suka maye gurbinta da Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *