
Jam’iyyar APC ta bayyana Jam’iyyar hamayya ta PDP da cewa Jam’iyya ce wadda aka kusa mantawa da ita saboda irin rikice-rikicen da Jamhuriyar ke fama dasu na cikin gida.
APC ta yi roko ga ‘yan Najeriya da cewa, kada su bari PDP ta dawo kan mulki musamman saboda la’akari da irin lalata kasarnan da suka yi a shekaru 16 da suka yi suna mulki.
Me magana da yawun Jam’iyyar ta APC, Bala Ibrahim ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da jaridar Punchng inda yace har yanzu barnar da PDP tawa Najeriya bata kare ba.
Jam’iyyar bata iya gudanar da komai ba hadda ma gudanar da kanta kamar yanda Bala Ibrahim ya fada inda yace abin dariya yake basu a APC.