
Ƴanbindiga sun kashe mutum uku, ciki har da jami’an tsaron Najeriya biyu a wani da suka kai a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Jigawa ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙaramar hukumar Ringim a jiya Laraba da marece.
Hukumar ta ce ƴan bindigar sun buɗe wa wasu jami’an sa-kai masu yaƙi da masu garkuwa da mutane wuta a ofishinsu.