
Wasu da ake zargin ƴan fashin jeji ne sun kai hari garin Faruruwa da ke Karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da ba a bayyana adadinsu ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a kasuwar garin da misalin karfe 7 na dare a jiya Alhamis, inda suka fara harbe-harbe kan me uwa da wabi.
Wani shaida, Ibrahim Faruruwa, ya ce maharan sun yi yunkurin sace wani hamshakin dan kasuwa, Alhaji Haruna Halilu, sai dai ba ya shagon nasa a lokacin harin.
Ya ce: “Da basu samu Alhaji Haruna ba, kawai sai suka sace dansa, Mas’ud.”
Ya kara da cewa maharan sun kashe mutane biyu — wato Alhaji Rabiu Faruruwa da Sahabi Dankwaro a yayin harbe-harben da su ka riƙa yi.
Wani mazaunin garin, Abubakar Hamza Adam, ya ce dan uwansa karami, Zunnurain, ya samu rauni a yayin harin.
Ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. ’Yan bindiga sun kai hari a Faruruwa, Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano. Wasu mutane sun mutu, wasu kuma an sace su.
“Dan uwana Zunnurain ya ji rauni a hannunsa, sannan an kwace masa wayar salula.
“Allah ya kare rayukanmu da dukiyoyinmu, ya kuma hana faruwar hakan a gaba.”
Da Daily Nigerian ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yansandan jihar, Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya ce zai bincika lamarin sannan ya sanar da wakilin ta, amma har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto, bai dawo da bayani ba.