
Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi Mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara.
Maharan sun kuma kashe akalla mutum 6, inda suka sake kai wani hari a yankin karamar hukumar Dandume ta jihar.
Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita bah ar zuwa ranar Lahadi da rana.
Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Garaa ne na ƙaramar hukumar Funtua, kuma ya ce ”Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ƴanmata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53”
”Sun kashe mutum 2 a Layin Garaa na ƙaramar hukumar Funtua da kuma wasu mutum 4 garin Mai Kwama a cikin ƙaramar hukumar Dandume.” In ji Malam Ya’u.
Shi ma maigarin Layin Garaa, Mustapha Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutanen sa na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, kwatsam kuma sai ga wannan matsala ta harin ƴanbindiga.
”Gwamnati tana ji tana gani wani abin ba a yi mana. Sojoji ma yadda ake turowa mu bamu samu gatan an turo mana su ba, ƴansandan da suka zo sai dai suka wuce suka nufi gardawa.” In ji Mustapha Abdullahi.
Matsalar tsaron dai ta tilastawa mutanen yankin yin hijira da ɗan sauran abubuwan da suka rage masu, kamar yadda maigarin Layin Garaa ke cewa.
Hukumar ƴansanda a jihar ta Katsina dai ta ce tana kan bincike a kai lamarin, domin haka ba za ta ce komai ba sai ta kammala.
Matsalar tsaro na ci gaba da zama ƙarfen ƙafa a jihar Katsina, kuma yayin da al’ummar da abin ya shafa ke ƙorafi da neman hukumomi su tashi tsare wajen ba su kariya, gwamnati da sauran jami’an tsaro na cewa suna bakin ƙoƙarin su wajen magance matsalar.