
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta kama wani matashi da ya ƙware wajen kwaikwayon muryoyin wasu gwamnonin Najeriya.
Ƴansandan na zargin matashin da amfani da muryoyin wajen damfarar mutane maƙudan ƙuɗaɗe.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa dama rundunar ƴansandan jihar ta jima tana neman matashin ruwa a jallo.
”Bayan kama shi mun same shi da lambobin waya da dama ciki har da na manyan mutane a ƙasar nan”, in ji kakakin ƴansandan.
”Mutumin ya ƙware sosai wajen kwaikwayon muryoyin mutane, duk wani mutum da ba ka tunani zai iya yi maka muryarsa”, in ji shi.