Sunday, August 16
Shadow

Ƴansandan Kaduna sun kama mai kwaikwayon muryoyin gwamnoni

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta kama wani matashi da ya ƙware wajen kwaikwayon muryoyin wasu gwamnonin Najeriya.

Ƴansandan na zargin matashin da amfani da muryoyin wajen damfarar mutane maƙudan ƙuɗaɗe.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa dama rundunar ƴansandan jihar ta jima tana neman matashin ruwa a jallo.

”Bayan kama shi mun same shi da lambobin waya da dama ciki har da na manyan mutane a ƙasar nan”, in ji kakakin ƴansandan.

”Mutumin ya ƙware sosai wajen kwaikwayon muryoyin mutane, duk wani mutum da ba ka tunani zai iya yi maka muryarsa”, in ji shi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wani barawo me Qarfin Hali ya sace Tirela guda ta Rake zai gudu, saidai wani soja ya Hhàrbì tayar motar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *