Sunday, January 12
Shadow

Ɓangaren Aminu Ado Bayero ya ce zai ɗaukaka ƙara

Bangaren sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ta yanke kan dambarwar masarutun jihar.

A ranar Juma’a ne kotun ɗaukaka ƙara ta yankee hukuncin cewa babbar kotun tarayya – da ta yi hukuncin dakatar da gwamnatin Kano daga soke masarautun jihar – ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi masarautu a jihar.

To sai dai a wani taron manema labarai da Aminu Babba Dangundi – wanda tun da farko ya shigar da gwamnatin Kano ƙara a madadin masarautun da aka rushe – ya yi, ya ce za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon wasu na rokon Kabarin Shehu ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur ya dauki hankula

Ya ce tun da farko gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar ba su bi ƙa’ida ba wajen soke masarautun jihar.

‘’Bai kamata a sauke sarki ba tare da ba shi damar kare kansa daga laifin da aka zarge shi a kai ba’’, in ji shi.

Ya ce tun a ranar da aka yanke hukuncin suka buƙaci kotun ta ba su kwafin takardun hukuncin, kuma a gobe Litinin za su garzaya gaban kotun ƙolin ƙasar domin ɗaukaka ƙarar.

A ranar Asabar ne dai gwamnatin Kano ta buƙaci ɓangaren Aminu Ado ya yi biyayya ga hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar.

To sai dai Aminu Babba ya ce Idan aka yi hukunci, kuma aka ɗaukaka ƙara to akan tsaya ne a matsayin da ake har sai kotun ta yi hukunci kan hakan.

Karanta Wannan  Tinubu dan uwanmu ne Bayerabe mun fi kowa sanin halinsa shiyasa bamu zabeshi ba a zaben 2023>>Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta magantu

‘’Saboda ita kotun ɗaukaka ƙara ba ita ce ƙarshe ba, akwai kotun ƙoli – wanda daga ita kuma shikenan dole a yi biyayya da hukuncinta’’, in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *