Thursday, February 6
Shadow

Sojoji sun ce sun lalata sansanin Bello Tùrjì tare da kkashe ‘yànbìndìgà 25

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar lalata sansanin gawurtaccen ɗan bindigar nan Bello Turji a yankin Fakai na ƙaramar hukumar Shinkafi.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar da ke yaƙi da ‘yanbindiga a arewa maso yamma ‘Operation Fansan Yamma’ ya fitar, ya ce dakarun sojin sun ƙaddamar da hare-haren ne kan maɓoyar ‘yanbindigar a ranar 10 ga watan Janairu.

”Bisa taimakon dakarun sojin sama, mun samu nasarar lalata sansanonin wasu ‘yanbindiga a yankin Fakai na ƙaramar hukumar Shinkafi”, in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa daga cikin sansanonin da aka lalata har da na Bello Turji da Mallam Ila, inda aka kashe ‘yanbindiga 25 tare da raunata fiye da 18.

Karanta Wannan  Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Haka ma ya ce a lokacin samamen sojojin sun kuɓutar da mutum bakwai da ‘yanbindigar suka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *