
Kungiyoyin fafutuka a Najeriya da suka hada dana Kwadago da sauransu sun bayyana aniyar fara zanga-zanga akan karin kudin kiran waya da kaso 50 cikin 100.
Sauran kungiyoyin da suka goyi bayan wannan zanga-zangar sun hada da HURIWA,JAF da NASU ta ma’aikatan jami’o’i.
Kungiyoyin sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su shiga wannan zanga-zangar a yi dasu dan nuna rashin jin dadin karin kudin kiran.
Hakanan itama kungiyar SERAP ta bayyanawa hukumar sadarwa, NCC cewa zata kai kara kotu kan lamarin.
Saidai NCC din ta yi kira ga kungiyoyin da su zo a yi zaman fahimtar juna dan ta yi bayanin dalilin da yasa aka yi wancan karin.