Monday, December 16
Shadow

‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin.

Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta haramtawa 'yan mata 'yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Ya kuma bayyana cewa nan da makwanni uku za a bude shafin neman bashin ga daliban da ke manyan makarantu na gwamnati domin su samu su iya cike takardun neman bashin karatu biyo bayan korafe-korafen da daliban suka yi.

Sawyerr ya kuma buƙaci shugabancin manyan makarantun gwamnati da su fara miƙa bayanan dalibansu domin tabbatar da tsarin bayar da bashin cikin sauƙi.

A ranar 12 ga Yuni, 2023 ne Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu saboda ɗalibai marasa galihu su iya yin karatu a manyan makarantun ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *