Saturday, August 8
Shadow

Matar Tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta bayyana kayan aikinta da ICPC suka dauka da suka je bincike gidan mijinta wanda a tunaninsu shine na’urar yiwa waya kutse

Matar tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta wallafa a shafinta cewa, ICPC sun dauke mata na’urar da take amfani da ita a banki.

Tace tana rantsuwa da Allah na’urar ba ta kutsen waya bace.

Ta bayyana cewa, cikin kayan da ICPC suka bayyana cewa sun dauka daga gidan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, sun manta su bayyana wannan na’urar tata.

ICPC dai sun bayyana wayoyi da kwamfutocin tafi da gidanka a matsayin abubuwan da suka gano a gidan malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Duk Wanda Ya Taimakawa Sòjin Nàjeriya Da Bayanaɲ Sirri Wajen Ganin An Kawo Ƙarshen Ƴan Biɲdíĝa, Zamu Bashi Kyautar Miliyan 20, Céwar Ƙarmin Ministan Tsaro Bello Matawalle

A baya kuma sun zargi cewa, sun gani na’urar yiwa waya kutse.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *