Monday, December 16
Shadow

20 daga Yaran da Gwamnatin tarayya ke tsare dasu bisa tuhumar cin amanar kasa zun kwanta rashin lafiya

Rahotanni sun bayyana cewa akalla 20 daga cikin yaran da gwammatin tarayya ke tsare dasu bisa zargin cin amanar kasa sun kwanta rashin lafiya.

Rahoton yace tuni aka garzaya da yaran zuwa Asibiti.

Tun da fari dai da aka kai yaran gidan yarin Kuje dake Abuja,hukumomin gidan yarin sun ki amincewa su ajiyesu.

Hakan yasa dole hukumar ‘yansandan Najeriya suka koma suka ci gaba da tsare yaran a inda suke tsare da manyan mutane.

Zuwa yanzu dai ba’a san wane asibitine aka kai yaran dan kulawa dasu ba.

Shuwagabannin zanga-zangar Take it back Movement dai sun je dan kaiwa yaran abinci da kayan sawa amma sai guda 6 kawai suka tarar a tsare inda aka sanar da su cewa sauran suna Asibiti.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Matashiya ta hau gini me tsawo ta fado ta mùtù bayan da aka hanata shigar banza a kasar Iràn

A baya dai hutudole ya kawo muku cewa, shugaban ‘yansandan Najeriya yace faduwar da yaran suka yi a kotu karyace kawai dan su ja hankalin mutanene.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *