
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai a gobe Talata ne za a yi jana’izar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya rasu ranar Lahadi a birnin Landa.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatinsa , Radda ya ce ya yi magana da iyalan tsohon shugaban ƙasar da kuma makusanta da ke Landan dangane da shirye-shiryen ɗaukar gawar zuwa Najeriya.
”Daga tattaunawar da na yi da iyalansa da makusantansa da ke tare da gawar, sun bayayna mana cewa ana ci gaba da shirye-shiryen yadda za a ɗauko gawar zuwa Najeriya”, in ji Gwamnan.
”Bayannan da na samu shi ne sai gobe da rana misalin ƙarfe 12:00 gawar za ta ƙaraso, don haka za a guanar da jana’izar da misalin ƙarfe 2:00 na ranar gobe Talata”, in ji gwamnan na Katsina.
Ya ƙara da cewa za a yi jana’izar tsohon shugaban ƙasar ne a mahaifarsa da ke Daura a jihar.
Tuni dai gwamnatin jihar Katsina ta ayyana yau Litinin a matsayin ranar hutu domin nuna alhinin kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar.
Ya zuwa yanzu iyalai da dangi da masu alhini sun cika gidan marigayin da ke garin Daura domin jiran isowar gawarsa.
Al’ummar garin Daura sun bayyana alhinin da suka shiga sakamakon asuwar tsohon shugaban na Najeriya.
Wasu daga ciki da BBC ta tattauna da su, sun yi addu’ar Allah ya yafe wa shugaban ƙasar.
Darkta Hajjo Sani, wata makusanciyar marigayin – wadda kuma ta yi aiki a matsayin babbar mai taimaka masa kan harkokin mulki, kafin ya naɗa ta wakiliyar Najeriya a hukumar Unesco ta bayyana shi da mutum mai kishin ƙasa da gaskiya da riƙon amana.
”Mutum ne maras son kai, wanda ya ɗauki duka ƙabilun Najeriya a matsayin ɗaya”, in ji shi.
Dakta Hajjo Ta ce Buhari Mutum ne da zai iya sayar da rayuwarsa domin gina Najeriya.
”Mutum ne mai faɗa da cin hanci da rashawa a Najeriya, kuma kowa zai iya shaida haka”, in ji ta.
A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa birnin Landan domin raka gawar marigayin zuwa Najeriya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya aike da umarci Shettima ya tafi Landan domin raka gawar marigayin.
Mataimakin shugaban ƙasar ya isa ne tare da rakiyar shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila.
Sun kuma sami tarba daga Ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, da Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a filin jirgin saman Landan.
Tsoffin shugabannin Najeriya na aikewa da ta’aziyya
Tuni dai tsoffin shugabannin ƙasar da suka yi ta aike wa da saƙonnin ta’aziyyar rasuwar marigayin, suna masu bayayna shi da mai kishin ƙasa kuma dattijo.
Tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo ya bayyana rasuwar Buhari a matsayin babban rashi ga Najeriya, ba ga iyalinsa kaɗai ba.
Shi ma tsohon shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar ibarhaim babangida mai ritaya, ya bayyana Buhari da mutum mai kyawawan halaye, kuma mai kishin ƙasa.
Haka shi ma shugaban ƙasar da Buhari ya kayar a zaɓen 2015, GoodLuck Jonathan ya bayyana marigayin da mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga aikinsa kuma ya yi wa Najeriya hidima.