Cikin ɗaren jiya ƴan ta’àďďa sun shiga ƙauyen Gidan Boka dake ƙaramar hukumar Malumfashi, sun ɗauki mutum ɗaya tare da kore shanu, amma jama’an gari sunmyi kukan kura sun bi su suka yi ta fafatawa da da su da bindìģùñ su na gida ƙarshe har saida suka fatat’taki ƴan ta’aďďan kuma suka kwace shanu da mutanan da suka ɗauka.
Shugaban hukumar tsaro ta ƴan sanda na garin Malumfashi S.P: Bello Umar, ya yi yabo da jinjina ga wannan jarumta da mutanan garin suka nuna wajen yin ƙoƙarin iya fito na fito da ƴan ťa’aďďan, kuma suka fafata da su har suka samu nasara ta kwace shanun da suka ɗauka da ceton mutumin da suka ɗauka duk a cikin daren, tun kafin ƴan sanda su kai ga isowa.
Haƙiƙa wannan ba ƙaramar nasara bace kuma abun koyi ne a gare, mu dukka al,ummah, nadade ina fadi mutane murinƙa ƙokarrin tashi tsaye da jarumtar tunkarar miyagun mutanan, nan ayayin da munkaji alamun sun shigo yan kunan,mu dan kawo manna hari, insha Allahu cikin taimakon Allah zakuga munyi nasara akansu, tun kafin kawo agajin hukumar tsaro.
Ƴan ta’ďďan dai sun shiga garin na Gidan Boka dake wajen garin Marmara, dake cikin ƙaramar hukumar Malumfashi jihar Katsina, da misalin ƙarfe 02:00 na daren jiya Talata.10/09/2024.
Daga It’z Kamalancy