Thursday, October 3
Shadow

Gyaran fuska da tafarnuwa

Tafarnuwa na da matukar amfani musamman a wajan gyaran fuska.

Ana amfani da tafarwa dan kawar da kurajen fuska da duk wani dattin fuska,hakanan amfani da ita a fuska yana maganin abubuwan dake kawo saurin tsufa.

Hakanan Tafarnuwa na disashe girman tabo a fuska.

Masana kiwon Lafiya sun bayyana cewa, goga Tafarnuwa a kan kurajen fuska yana taimakawa sosai wajan magance kurajen.

Saidai a bi a hankali, Tafarnuwa na sawa a ji zafi ko kaikayi a yayin da aka sa ta a fuska.

Ba kowane tafarnuwa za iyawa aiki ba, saboda wasu idan suka shafata a fuskarsu, zata iya yi musu illa sosai wajan sa kai kai ko zafi.

Dan haka a shawarce, a dan shafata a wani bangare kadan na fuska a ga yanda zata yi, idan ba’a ji ko mai ba, sai a shafa a sauran duka fuskar.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da kurkur

Hakanan yana da kyau a hada tafarnuwar da man kwakwa ko man zaitun, hakan yana rage zafi ko kaikayin da zata iya sawa a fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *