Wednesday, January 15
Shadow

Tuwon madara mai kwakwa


Yanda ake Tuwon Madara me kwakwa da butter.

Abubuwan da ake bukata:

Madara Loka 2:

Ruwa Karamin Kofi 3.

Sai Sugar Gwangwani 4.

Sai Butter Leda daya.

Sai Vanilla.

Robar Kwabi.

Kwanon Suya.

Muciya.

Farantin Silver.

Karamar wuka.


Da farko ana kankare kwakwa( wasu suna fara kankare bayan kwakwar su fitar dashi ya zama saura farin kwakwar kawai, wasu kuma basa kankarewa) se a sata a kasko a soya ba tare da an zuba mai ba, sama-sama za’a soya kada a bari tayi ja.

Se a sauke na a dora kason a sa ruwa karamin glass cup uku, ko kuma karamin kofin roba uku se a zuba sugar gwangwani hudu saboda madaran Loka biyu ce.

Karanta Wannan  Yadda ake tuwon madara

Da sugar din ya dahu yayi kauri Se a zuba kwakwan a ciki sannan a zuba butter a barshi ya dan kara dahuwa kadan.

A gefe guda kuma sai a samu roba ko kwano me kyau a zuba madarar, sannan a zuba mata Vanilla a juya su hade da kyau.

Sannan sai a dakko ruwan sugar din da aka dafa tare da kwakwa da Butter a zuba a cikin madarar a yi ta juyawa har su hade sosai.

Sai a samu bayan tire na silver a rufe da leda a zuba kwabin akai a samu muciya a bazashi daidai kaurin da ake so sai a yayyanka.

Shikenan sai a ci dadi, idan kuma na sayarwa ne sai a fara sayarwa dan komai ya kammalu.

Karanta Wannan  Yadda ake kunun gyada

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *